Game da Mawallafi

Abi benson Silon an haife shi ne a Silon na Karamar hukumar Song a Jihar Adamawa ta Nijeriya. Ya halarci sashin karatun sa na farko a Firamare School na Silon kuma ya kare ta a 1993/1994.

Ya kuwa tafi Secondary School na farko a Dumne  daga 1994-1997.

Ya kuma sake komawa baya a aji Biyu na junior a Song (GJSS) da aka sani a da da suna Kwalejin horas da Mallamai (TC) a 1998-1999. Daga nan ne ya sake komawa a GDSS Dumne ya shiga Siniya Sakandari kuma ya je ya kare a Siniya Sakandari na Song inda yake a da. Ya kuwa kare a 2003. 

Ya kuma tafi Kwalejin Horas da Mallamai a (COE) Hong a 2006-2009 inda ya sami NCE cikin nazarin yarurukan Turanci da Hausa. Ya sami aikin koyarwa da a Sakandari School da Gwamnatin Adamawa a shekara ta 2010/2011. Bayan wannan sai inda ya tafi Digiri na farko a Evangelical Theological Seminary Kaltungo a 2016 domin samun B.Arts na ilimin addinin Krista inda ya iso kashi na 300 sai ya nemi takardar karatu a Kwalejin Tauhidi na Arewancin Najeriya da ke Bukuru Jos domin karanta Fannin yaruruka da juya littafi Mai Tsarki zuwa wassu yaruruka, sai ya tafi a 2008-2022 (B.Arts).

Your encouragement is valuable to us

Your stories help make websites like this possible.