Bambambace-bambamcen Harsunan Mboi

Manyan Garuruka da Kauyukan da ke ɗauke da Harsunan

Mboi a masayin ta na Kabila tana da manyan harsuna mabambanta kashi biyu (Mboi da Handa kamar yadda na shaida ta wurin kasancewa ta kusa da al'ummar mboi na shekaru kusan ashirin. ko da shike Blench (2019) yace Kabilar tana da  harsuna har guda uku (Mboi, Handa da kuma Banga). Bisa nasa, Handa tana masa kamar wata Kabila ce dabam. Bisa ga binciken Abi da kuma sanadiyar zama kusa da Kabilar na kusan shekaru ashirin da kuma yin lura, haɗe da yadda dattawa masu yaren sun bada tabbacin haka, yaren tana da harsuna mabambanta guda biyu ne kaɗai. Domin wannan, Mboi sunar kabila ce kuma sunan ɗayan harshe ce, sa'annan Handa wanda ta kunshi hatta Banga a ciki duk da cewa da 'yan bambance-bambance. 

Rabe-raben harsuna mabambantan suna nan kamar yadda take a kasa.

  1. Mboiː Sigire, Golontaɓal, Baawo, Nadɗa, Ɓokki, Mbilla, Garintuwo, Bwarangai, Livo, Gulgul, Kesure, Zangra, Baitalami, Gakta, Daɗe, Murvəci, Gulungo, Garin Mission, Gejeli, Gerwel, Perwel, Lewa, Kəngo, Moddo, Shitto, Wuro modi, Jambutu, Kasamən, Kwayar, Bishi, Bumbo, Wantoro, Dame, Wuro Yeso, Baranga, Wurcibca, Kance, and Cikkol.

2. Handaː Harshen Handa kuma ta haɗa da,Banga, Handa, Kuɓa, Bnne, Zne, Kaulara, Zumbe, Diɓade, Ɓundu.

Akwai wassu 'yan kananan bambance-bambance kamar yadda an faɗa tun daga farko. Bambance-bambance na harsunan Mboi da Handa suna nan a fili ga wanda ya zauna a sakanin su na sawon makwanni biyu bisa ga lura irin ta nazarin yaruruka. Mai nazarin nan yayi amfani da harshen yungur wurin kwatanci domin samun karin bayani. Wannan kasafi da ke kasa na nuna waɗansu bambance da ke sakanin harsunan guda biyu ɗin na yaren Mboi dangane da yaren da ke kusa da ita. 

 Mboi                                   Handa                Yungur    Ma'anarsa a Hausa
1    Mbiya                                 Mbəra              Mbərã       ruwa
2    Kitiya                                 Kucira         Kəra                  karan hatsi
3    Pitiya                                  Picira          Mbukəfa          abinci
4    Semfandayau?    Semfandərau?    Sokolosəreu?    ba haka ba ne?
5    Hayau?                               Harau?       Losau?              haka ne?
6    Pitiya    picira                   Pira,            ɓura                   kunu

Domin karin bayani, tuntuɓi marubucin.

www.abensonabi@tcnn.edu.ng   or +2347082815338

Your encouragement is valuable to us

Your stories help make websites like this possible.